Jami’in Kungiyar Hamas Ya Ce; Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba Ta Ga Karyewar Zuciya Daga Al’ummar Falasdinu Ba

Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ba ta ga wani rauni ko karyewar zuciya daga al’ummar Falasdinu ba, kuma ta samun tabbacin

Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ba ta ga wani rauni ko karyewar zuciya daga al’ummar Falasdinu ba, kuma ta samun tabbacin ba za ta iya yin galaba a kan al’ummar Falasdinu da ‘yan gwagwarmaya ba

Babban jami’i a ofishin siyasar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas kuma shugaban kungiyar a Zirin Gaza, Khalil Al-Hayya  ya bayyana a yammacin jiya Laraba cewa: Abin da ya faru a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, wani abin al’ajabi ne da kuma nasara ce ga soji da tsaro da kuma manyan bangaren sojin dakarun Izzuddeen Al-Qassam da suka samu kan makiya ‘yan mamaya. Sannan ‘yan gwagwarmaya za su ci gaba da zama abin alfahari ga al’ummarsu da daukakan gwagwarmayar a fagen rayuwa wanda zai ci gaba da gudanar al’umma bayan al’umma, kuma ba za a yi shaidan samun rauni ko rashin nasara daga wannan al’ummar ba.

Shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada labaran Falasdinu ya bayyana cewa: Al-Hayya ya jaddada hakan ne a wani jawabi da ya yi gabatar kan cimma yarjejeniyar dakatar da yakin da ake yi a Zirin Gaza, inda ya bayyana cewa: Harin daukan fansan Ambaliyar Al-Aqsa ya yi mummunar barna ga makiya ‘yan sahayoniyya, kuma zai ci gaba da kasancewa babban abin kunya a kansu da al’ummun da suka yi shiru kan zaluncin da aka aiwatar kan al’ummar Falasdinu. Yana mai jaddada cewa; Al’ummar Falasdinu ba zasu taba manta wadanda suka taimaka wajen aiwatar da wannan ayyukan dabbancin kan su ba, yana mai jaddada cewa: Tabbas makiya ba su ga wata alamar rauni da karyewar zukata daga al’ummar Falasdinu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments