Jami’an Leken Asirin “Shabak” Na Isra’ila Sun Kama Nasir Lahham Na Tashar Talabijin din Almayadin

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida, “Shabak” ta kama shugaban ofishinta a Falasdinu dake karkashin

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida, “Shabak” ta kama shugaban ofishinta a Falasdinu dake karkashin mamaya  Nasir al-Lahham, a gidansa da yake a garin Beithlaham.

Majiyar ta kara da cewa; Jami’an kungiyar leken asirin ta “Shabakh” sun dade suna binciken dakin watsa labarin da Lahham yake watsa shirye-shiryensa.

Tashar ta “Almayadin’ dai ta bayyana cewa kamun da aka yi wa ma’aikacin nata yana a karkashin Takura mata ne da HKI take yi, domin a cikin watan Oktoba na 2023 ma dai jami’an tsaron sun kai hari cikin gidansa, su ka ci zarafin maidakinsa da kuma kama ‘ya’yansa Basil da Baasil.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted