Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Al’umma zata ji labari mai dadi game da daukar fansan Iran kan haramtacciyar kasar Isra’ila
A jawabin da ya gabatar a wani taron jama’a a mashigar kasa da kasa ta Khosravi da ke yammacin kasar Iran, kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husain Salami ya dauki alkawari tare da jaddada yin bushara kan yadda Iran zata dauki fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Manjo Janar Salami ya ziyarci mashigar kasa da kasa da ke Khosravi ne tare da rakiyar kwamandan hedikwatar Najaf Al-Ashraf, Kwamanda da mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na lardin Nabi Akram (s.a.w) da mataimaki a harkokin siyasa da tsaro nalardin, da sakataren kwamatin tattakin Arba’in na Imam Husaini{a.s}, da wasu jami’ai da dama a lardin don duba zirga-zirga da dawowar baƙi da suka kai ziyarar ranar Arba’in.
Yayin da ya kai ziyara a kofar shigewar masu ziyara, Manjo Janar Salami ya zanta da jama’a a mashigar, inda ya kuma yi musu bayani kan yanayin zirga-zirga da kuma matsalolin da ke tattare da hanyar. Da yake amsa tambayar da mutane suka yi game da ramuwar gayya kan haramtacciyar kasar Isra’ila, ya ce za ku ji labari mai dadi game da daukar fansar, idan Allah Ya yarda.