Jami’ai 12 da suka yi murabus daga gwamnatin Biden sun soki manufofinsa game da Gaza

Jami’ai 12 da suka yi murabus daga gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden saboda yakin Gaza sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa da ke

Jami’ai 12 da suka yi murabus daga gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden saboda yakin Gaza sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa da ke nuni da gazawar manufofin Biden kan yakin da Isra’ila take kaddamarwa a kan al’ummar Gaza.

A cikin sanarwar da Jami’an da suka yi murabus daga gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden saboda yakin Gaza suka fitar, sun yi kira ga jami’an da suka rage a cikin gwamnatin da su “kalubalanci shugabanninsu kada su bari a yi amfani da su wajen aiwatar da manufofin kisan bil adama.”

Jami’an, wadanda a baya suka yi murabus daga mukamansu, saboda tsarin da Biden ya dauka, a cikin  sanarwar hadin gwiwa ta farko da suka yi, sun ce manufar gwamnatin Biden kan Gaza ” barazana ce ga tsaron kasar Amurka,” tare da bayyana matakan da suka dace a dauka don sauya alkibla, kamar yadda shafin yanar gizo na kasar Amurka “HuffPost” ya bayyana.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Manufar Biden kan lamarin Falastinu musamman Gaza ba mai kyau ba ce ga Amurka da al’ummarta, kuma “ta kasance mai barna ga al’ummar Palasdinu, wanda ya haifar da mummunan yanayi na talauci da yanke kauna, tare da dukkanin abubuwan da ke faruwa ga al’ummomi masu zuwaa a nan gaba, sannan suka bayar da wasu shawarwari kan yadda za a magance wannan matsala.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments