Kasar Iran Zata Mayar Da Martani Kan Yahudawan Sahayoniyya A Lokacin Da Ya Fi Dacewa

Memba a Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Matakan da Iran zata dauka wajen mayar da martani kan haramtacciyar kasar

Memba a Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Matakan da Iran zata dauka wajen mayar da martani kan haramtacciyar kasar Isra’ila zasu kasance wadanda aka yi zurfin nazari kansu

Mohsin Reza’ei, memba a Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci ta kasar Iran, ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi nazari kan sakamakon hukuncin da zata yanke, kuma ba za ta bar Benjamin Netanyahu ya fice daga mummunar kangin ya shiga ba ta hanyar amfani da yanayin yanki ba.

A cikin wata hira da tashar talabijin ta CNN ta Amurka: Mohsen Reza’ei ya kara da cewa: Mafita daya tilo da za ta tabbatar da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya ta ta’allaka ce ga samun hadin kan kasashensu.

Mohsen Reza’ei ya kuma jaddada cewa: Dole ne a tsagaita bude wuta a Gaza kuma dole ne a hukunta Netanyahu a kotun kasa da kasa dake hukuntan manyan laifuka a duniya.

Mohsen ya kara da cewa: Iran za ta mayar da martani ga haramtacciyar kasar Isra’ila a daidai lokacin da ya dace da kuma wurin da yafi dacewa, domin haramtacciyar kasar Isra’ila zata ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri matukar ba ta fuskanci mayar da martanin mai gauni ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments