Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da harin ta’addanci da aka kai a ranar Talata a yankin Tillaberi na jamhuriyar Nijar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkata wasu sojoji da fararen hula.
Kan’ani ya jajantawa gwamnati da al’ummar Nijar, musamman ma iyalan wadanda wannan mummunan hatsarin ya rutsa da su, inda ya jajanta musu.
Kan’ani ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana daukar ta’addanci a matsayin babbar barazana ga al’ummomi da tsaron kasa da kasa, tare da jaddada wajabcin hadin kai da kuma kokarin da kasashen duniya suke yi na tunkarar wannan barazana ta bai daya.
Sojoji 20 da farar hula 1 ne aka kashe a yammacin Nijar da ke fama da hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda, in ji ma’aikatar tsaron kasar a ranar Talatar da ta gabata.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta gidan talabijin na kasar ta ce, hadin gwiwar kungiyoyin ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai hari kan jami’an tsaro a kusa da garin Tasya, inda suka kashe mutane 21 ciki har da farar hula guda, tare da raunata wasu tara na daban.
An kuma bayar da rahoton cewa: An kashe da dama daga cikin maharan, kuma an tura sojojin sama da na kasa domin murkushe wadanda suka gudu daga cikin ‘yan ta’addan.