Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Karfafa Alaka Da Kasashen Nahiyar Afirka

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran za ta cigaba da aiwatar da burin marigayi shugabanta da ministan harkokin wajensa na ganin ta

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran za ta cigaba da aiwatar da burin marigayi shugabanta da ministan harkokin wajensa na ganin ta karfafa alaka da kasashen nahiyar Afirka 

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani ya bayyana cewa: Matsayi da hangen nesa na shugaban kasar Iran marigayi shahidi Sayyid Ibrahim Ra’isi da ministan harkokin wajen kasarsa shahidi Hossein Amir Abdollahian, wadanda suka dogara kan ci gaba da kokarin zurfafa da kuma daukaka matsayin alakar Iran da kasashen Musulmi musamman Jamhuriyar Masar, za su ci gaba duk da rasuwarsu.

Jaddada wannan matsayin ya zo ne a yayin ganawar da aka yi a yammacin jiya Laraba a birnin Tehran, tsakanin Bagheri Kani da ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry.

Bagheri ya yaba da ziyarar da Shukri ya kawo zuwa Iran a madadin gwamnati da al’ummar Masar domin jajantawa da halartar taron tunawa da shahidai shugaban kasar Iran da mukarrabansa gami da isar da sakon Jami’ar -Azhar, wadda ta mika ta’aziyyarta kan wannan babban rashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments