Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Jaddada Cewa Dole Ne Iran Ta Dauki Fansa Kan Isra’ila

Jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Martanin Iran kan haramtacciyar kasar Isra’ila zai kasance mai matuƙar mamaki Jakadan Iran kuma wakilin

Jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Martanin Iran kan haramtacciyar kasar Isra’ila zai kasance mai matuƙar mamaki

Jakadan Iran kuma wakilin dindindin na kasar a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana dangane da lokacin da Iran za ta mayar da martani kan zaluncin yahudawan sahayoniyya da kuma kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas shahidi Isma’il Haniyeh a birnin Tehran, da cewa: Martanin Iran ga haramtacciyar kasar Isra’ila za ta kasance mai matuƙar ban mamaki.

Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya mayar da martani a ranar Laraba kan cewa ko Iran za ta jinkirta kai harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila har sai an ci gaba da shawarwarin tsagaita bude wuta, yana mai cewa: Tantance lokacin da Iran za ta mayar da martani mai gauni, zai zo ne lokacin da martaninta zai kasance mai matukar ban mamaki.

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Ya kamata martanin kasar Iran ya hukunta mai wuce gona da iri wajen kai harin ta’addancin da ya aikata da kuma keta hurumin kasar Iran da kuma karfafa karfin Iran wajen wurga haramtacciyar kasar Isra’ila cikin mafi girman nadama, don hakan ya zama abin da wurga yahudawan sahayoniyya cikin babban nadama da takaici.

Har ila yau, tilas ne martanin Iran ya kauce wa duk wani mummunan tasiri kan yiwuwar tsagaita bude wuta (a Gaza), kuma mai yiwuwa ne martanin Iran na iya kasancewa a cikin lokaci da yanayi da kuma yadda wannan hukuma azzaluma ta kasance tana ƙididdige mafi ƙarancin yiwuwarsa, watakila lokacin da idanunsu suke kula da sararin sama da na’urar rada, watakila martanin zai zo ne ta yadda ba su taba zato ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments