Jakadan Iran A MDDuniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau

Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai.

Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya.

Ya ce: “Maimakon amincewa da wannan tafarki na hankali, Amurka da Troika na Turai sun zaɓi haɓaka matsin lamba, da rarrabuwan kai.” Ya kara da cewa: “Wannan sabanin da ke tsakanin kalamansu da ayyukansu ya sake tabbatar da cewa hakikanin manufarsu ba ta diflomasiyya ba ce illa kara ta’azzarar matsaloli, don haka dole ne a yanzu su dauki cikakken alhakin rikicin da su kansu suka haifar.”

Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matakin da kwamitin sulhun ya dauka a yau a matsayin mai gaggawa, wanda bai dace ba, kuma ya sabawa doka. Iran ba ta ganin wajibcin aiwatar da ita. Yana mai jaddada cewa “alhakin mummunan sakamakonsa ya rataya ne kacokan ga Amurka da kungiyar Troika ta Turai, wadanda suka kirkiro zargin karya kan Iran tare da ba da damar kai hare-hare da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a kan cibiyoyi masu kariya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted