Kasar Afirka Ta Kudu ta ga yadda Palasdinawa suka jajirce wajen kare kansu daga HKI ne, ya sa ta gurfanar da HKI a gaban kutun ICC don kawo karshen kissan kiyashin da yahudawan suke masu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kasar Afirka ta gudu dai tana dade tana goyon bayan masu gwagwarmayan neman yencinsu a duniya daga ciki da da kasar Falasdinu da aka mamaye. Har ila yau da kuma ganin tarihin da kasar take da shi, na yaki da wariyar launin fata a kasar, duk sun hadu sun karfafa ta wajen daukar wannan matakin kan HKI.
Jakadan kasar Afirka ta kudu a nan Tehran, Francis Moloi ne ya fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Iran Press’ na kasar Iran a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa, wannan dan kadan Kenan daga abinda kasar Afrika ta kudu za ta iya gabatarwa da karfafa wa al-ummar Falasdinawa.
Yakin gaza dai ya farkar da mutane da dama a duniya gaba daya, kan al-amarin Gaza da kuma yadda HKI ta ke amfani da dukkan karfinta a cikin watannin 15 da sukagabata don kashe Falasdinawa da kuma rusa yankin nasu gaba daya.
Kasashen duniya musamman ita Afrika ta Kudu ta dauki wannan matakin ne, saboda yadda HKI ta ki mutunta dokokin kasa da kasa, musamman wadanda suka shafi
mutuncin bil’adama da kuma hakkin rayuwa ga Falasdinaw.