Jagoran Juyin Musulunci Ya Bayar Da Tallafin Kudi Domin Sakin Fursunoni

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayar da tallafin kudin da sun kai Riyal biliyan 40 ga kungiyoyin agaji da suke

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayar da tallafin kudin da sun kai Riyal biliyan 40 ga kungiyoyin agaji da suke aiki domin ganin an saki frusunonin da su ka aikata laifuka ba cikin ganganci ba.

 A kowace shekara  a cikin watan Ramadan mai alfarma kungiyoyin na agaji suna kaddamar da neman taimako saboda sakin fursunonin da su ka aikata laifuka ba a cikin ganganci ba.

Ana amfani da kudaden ne wajen biyar  fansa da diyya ga wadanda fursunonin su ka yi wa illa. Biyan fansa din dai ana yinsa ne  maimakon zartar da hukunci na Kisasi.

Watan azumin Ramadana da shi ne na 9 a  cikin kalandar musulunci yana da matsayin na musamman da ake son aikata alheri fiye da kowane lokaci a cikinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments