Jagoran Juyin Musulunci ya amince da Masoud Pezeshkian a matsayin shugaban Iran na 9

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da Masoud Pezeshkian a matsayin sabon shugaban kasar Iran. A wani bikin da aka

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da Masoud Pezeshkian a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

A wani bikin da aka gudanar kuma aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin na kasar a yau Lahadi, Ayatullah Khamenei ya amince da Pezeshkian a matsayin shugaban kasar a hukumance, wanda ya  yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 5 ga watan Yuli.

Jami’an gwamnatin Iran da na soji, da malaman makarantun hauza da jami’a, da wakilan kungiyoyi daban-daban, da gungun iyalan shahidai, da jakadun kasashen waje a Tehran sun halarci bikin.

Shugaban ofishin jagoran ya karanta bayanin amincewar jagoran  da wa’adin shugabancin Pezeshkian a wurin taron.

A cikin wannan sanarwar, Ayatullah Khamenei ya ce: Jarrabawar tantance makomar zaben shugaban kasar ta zo karshe a natse kuma cikin kwanciyar hankali, sakamakon kokarin da mutane da jami’ai suka yi, kuma mutumin da al’ummar kasar suka zaba ya kasance a shirye ya dauki wani babban nauyi.”

Ya kuma bayyana zaben shugaban kasa karo na 14, wanda aka gudanar bayan wa’adin mulkin marigayi Ibrahim Raeisi, a matsayin daya daga cikin daukakar al’ummar Iran, kuma wata alama ce ta tabbatar da tsarin Musulunci mai dorewa wanda ke nuni da hankali da wayewar al’ummar kasar da sanin yanayi na  siyasar kasar.

Jagoran ya kuma bayyana fatan samun nasara ga Pezeshkian, inda ya kara da cewa kuri’ar al’ummar kasar da amincewarsu za ta dore matukar dai shugaban ya bi tsarin da ya ginu a kan  tafarkin  juyin juya halin Musulunci.

Pezeshkian zai yi rantsuware kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar ranar Talata.

Kwararren likitan zuciya mai shekaru 69 da haihuwa ya samu kuri’u sama da miliyan 16 a kan tsohon mai shiga tsakani na tattaunawar nukiliya Saeed Jalili, wanda ya samu sama da miliyan 13 daga cikin sama da kuri’u miliyan 30 da aka kada, yayin da yawan masu jefa kuri’a ya kai kusan kashi 50 cikin dari.

A cikin jawabin nasara, Pezeshkian ya bayyana nasararsa a matsayin farkon “sabon babi” ga kasar.

An kira zaben na gaggawa ne bayan shugaban kasar Iran Ibrahim Raeisi ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan Mayu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments