Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ziyarci Iyalan Shugaban Kasar Ibrahim Ra’isi

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya ziyarci iyalan marigayi shugaban kasar Iran shahidi Sayyid Ibrahim Ra’isi Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya ziyarci iyalan marigayi shugaban kasar Iran shahidi Sayyid Ibrahim Ra’isi

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci gidan shahidi Sayyid Ibrahim Ra’isi, inda ya tattauna da iyalansa masu girma a jiya Laraba.

Abin lura a nan shi ne cewa: Bayan sallar jana’izar da Jagoran juyin juya halin Musulunci yajagoranta a kan gawar shugaban shahidi Hujjatul-Islam Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa a safiyar yau jiya Laraba, an dauke gawarwakin tsarkaka daga dandalin juyin juya halin Musulunci zuwa dandalin Azadi a gaban idon miliyoyin ‘yan kasa.

Bayan kammala bikin kaddamar da madatsar ruwa ta “Giz Galasi” da ke kogin Aras da ke tsakanin kan iyakar Iran da Jamhuriyar Azarbaijan, wanda ya gudana a gaban shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da na kasar Azarbaijan Ilham Aliyev a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, Sayyid Ra’isi da tawagarsa sun kama hanyar birnin Tabriz da jirage masu saukar ungulu guda uku, domin kaddamar da wani aiki na inganta samar da matatar mai, amma jirgin mai saukar ungulu da ke dauke da shugaban kasar ya fado a sakamakon hadarin saboda mummunan yanayi da hazo mai yawa a yankin Varzagan na lardin Azarbaijan ta gabas ashiyar arewa maso yammacin Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments