A jawabin da ya gabatar a safiyar yau Laraba, a daidai lokacin da ake cika shekaru 36 da wafatin jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khumaini (Allah ya jikansa), Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a matsayin martani ga shawarar Amurka, ya jaddada cewa inganta sinadarin Uranium shi ne mabudin batun nukiliya, kuma ba za su taba yin watsi da shi ba.
A wajen wannan juyayi, bayan karatun kur’ani mai tsarki da yabon Ahlul-baiti (a.s) jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa inda ya ce: Kafin ya ce komai, yana mika jinjinarsa ga ruhin Imam mai girma da kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da ya daukaka darajarsa.
Jagoran ya kara da cewa: Gobe ne ranar Arafah, kuma mabudin Sallah, don haka yana nasiha ga matasa da yin sallah, su bayyana bukatunsu da manufofinsu ga Allah Madaukakin Sarki, tare da neman taimakonsa.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tsarin siyasarsu wanda alhamdulillahi ya samu ci gaba da karfafa shi ne sakamakon juyin juya hali mai girma, kuma jagoransu mutum ne mai girma wanda har yanzu ake jin kasancewarsa a duniya sama da shekaru talatin bayan wafatinsa, kuma har yanzu tasirin juyin juya halinsa a bayyane yake ga al’ummar duniya, kuma irin koma bayan da Amurka take da samu a duniya yana da nasaba da samuwarsa da kuma kiyayya da juyin juya halinsa.