Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: An yi galaba a kan yahudawan sahayoniyya, amma babban shan kashi yana ga kasashen yamma
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kasa murkushe gwagwarmaya, amma babban shan kaye yana ga al’adu da wayewa da kuma ‘yan siyasar kasashen yamma.
A yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki a taron tunawa da shahidai dubu 15 a lardin Fars: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la’akari da abubuwan da suke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya da yadda ‘yan gwagwarmaya suke tsayin daka da kuma yadda ‘yan gwagwarmaya suka kasance a matsayin wani dalili na sauya makoma da tarihin yankin.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Abubuwan da suke faruwa a wannan yanki da tsayin daka da jihadin ‘yan gwagwarmaya sun haifar da sauya makoma da tarihin yankin.
Ya jaddada gazawar yahudawan sahayoniyya wajen kawar da gwagwarmayar duk da kashe mutane sama da 50,000 da ba su ji ba ba su gani ba, yana mai la’akari da babban shan kashi shi ne makomar al’adu, wayewa da ‘yan siyasa na yammacin turai, inda ya kara da cewa idan aka kwatanta tsakanin bangaren gwagwarmaya da bangaren masu dauke da siyasar sharri za a ga bangaren ma’aunin ‘yan gwagwarmaya ya fi rinjaye. Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei ya kara da cewa abubuwan da suke faruwa a wannan yanki da suka hada da abin da ke faruwa a Gaza da Lebanon da kuma gabar yammacin kogin Jordan sun kafa tarihi.