Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Dole Ne A Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Netanyahu

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce: Fitar da sammacin kama Netanyahu bai wadatar ba, a maimakon haka, dole ne a kashe shi

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce: Fitar da sammacin kama Netanyahu bai wadatar ba, a maimakon haka, dole ne a kashe shi

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Ba a daukan luguden bama-bamai a kan gidajen fararen hula a matsayin nasara, don haka makiya ba su ci nasara ba, ko a Gaza ko a Labanon, kuma ba za su taba yi nasara ba, kuma abin da ke faruwa laifukan yaki ne, yana mai ishara da hakan, bayan fitar da sammacin kame fira ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya Benjamin Netanyahu da ministan yakinsane Yoav Gallant, yana mai jaddada cewa; Fitar da sammacin kama su ba ta isa ba, dole ne a kashe su.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fadi hakan ne a taron makon hadin kai na Iran, bayan karbi bakwancin dimbin masu fafutuka daga sassa daban-daban na kasar tare da halartar babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar a birnin Tehran.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da cewa; Samun hadin gwiwa wani lamari ne da ba a taba samun irinsa ba a kowace kasa ta wannan siga, kuma ba wai kawai a fagen soja ba, duk kuwa da irin muhimmancin da yake da shi, a’a, ya hada da wasu bangarori da suka hada da al’adu da na zamantakewa, waɗanda mahimmancinsu ba su kasa girman soja ba.

Ya yi nuni da cewa, wannan lamari ya samo asali ne daga al’adu da tarihin kasar Iran, kuma shi ne asali da tushe mai alaka da al’ummar Iran, tarihinsu da kuma asalinsu.

Jagoran ya bayyana cewa dakarun hadakar sun dogara ne da ginshikai guda biyu na imani da Allah da dogaro da kai, kuma suna da jaruntaka, fasahar kere-kere, saurin aiki, da sanin makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments