Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana wa shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas cewa: Alkawarin Ubangiji na kawo karshen yahudawan sahayoniyya zai cika
A yammacin jiya ne Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma’il Haniyyah wanda ya zo Tehran a madadin gwamnatin Falasdinu da al’ummarta domin jajantawa Jagoran juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran kan rashin shugaban kasa da ministan harkokin wajen kasar da mukarrabansu.
A cikin wannan zaman taro, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mika godiyarsa ga al’ummar Falastinu, musamman ma al’ummar Gaza bisa tausayawar da suka nuna, tare da taya murna da kuma jaje ga shahadar ‘ya’yan Isma’il Haniyyah, gami da yabo kan hakurin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas.
Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin gagarumin tsayin daka da al’ummar Gaza suka nuna, wanda ya bai wa duniya mamaki, yana mai cewa: Wane ne zai yi imani cewa wata rana za a din ga rera take a jami’o’in Amurka na goyon bayan Falasdinu, kuma za a daga tutar Falasdinu, kuma wane ne zai yarda cewa wata rana a Japan za a gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ana rera taken “Mutuwa ga Isra’ila” da harshen Farisanci.