Jagoran Juya Juya Halin Musulunci Ya Ce: Kungiyar Hizbullah Za Ta Bada Mamaki Ga Makiya

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Karfin kungiyar Hizbullah ya wuce yadda makiya yahudawan sahayoniyya za su yi nasara kanta A rana ta

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Karfin kungiyar Hizbullah ya wuce yadda makiya yahudawan sahayoniyya za su yi nasara kanta

A rana ta biyar ta makon tsaro mai tsarki Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin tawagar masu fafutuka a fagen jihadi da tsayin daka.

A yayin wannan taro, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: A                                                                                                                                                                                                                                              yau, albarkacin gwagwarmayar al’ummar Iran, makiya ba za su yi kuskure kai harin wuce gona da iri kan iyakokin kasar Iran ba, duk da cewa suna tsare-tsaren wasu yunkuri na daban domin cutarda kasar.

Jagoran ya yi nuni da cewa: Sabanin da makiya suke yi da Iran ba wai don batun nukiliya ba ne, ko hakkokin kare hakkin dan Adama, ko kuma hakkin mata ne kawai ba. Tsarin duniya bai iya lamunta da amincewa da bullar juyin juya halin Musulunci ba, duk da cewa Iran ba ta da karfin soja a wancan lokacin.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi nuni da cewa: Juyin juya halin Musulunci na Iran ya dauki wani sabon salo na kin mika wuya ga manyan kasashen duniya masu girman kai, Yana mai fayyace cewa: Mahukuntan duniya sun so kai wa Iran hari, sai suka samu azzalumi da baya da ruhin dan Adamtaka Saddam Hussein suka wakilta shi a madadinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments