Search
Close this search box.

Jagora Ya Yi Kira Ga Jami’an Iran Da Jira Makiya Sai Makiya Sun Amince Da Shirye-Shiryensu

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kada jami’an Iran su jira makiya sai sun amince da shirye-shiryensu, kuma kada su amince da yaudararsu

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kada jami’an Iran su jira makiya sai sun amince da shirye-shiryensu, kuma kada su amince da yaudararsu

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki makamashin nukiliya a matsayin daya daga cikin tsare-tsare masu muhimmanci ga makomar kasar a nan gaba, ya kuma yi watsi da wasu bayanai da suke da shakku kan fa’idojin da yake da shi, yana mai cewa: kasar ba za ta iya hana kanta samun ilmin kimiyya da fasaha na zamani a ci gaban wannan duniya ba, kuma daga baya ta koma bayan shekaru tana neman hanyar wannan ci gaban ba.

A ganawarsa da manyan jami’an gwamnatin Iran a yayin gudanar da bukukuwan “Makon Gwamnnati” a jiya Talata, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayayullahi Sayyid Ali Khamenei a farkon wannan zaman taro ya karrama shahidi marigayi tsohon shugaban kasar Iran Rajai da fira ministansa Bouhunar da kuma marigayi Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa.

Ayatullahi Khamenei ya yaba da gagarumin yunkuri da al’ummar kasar suka nuna na zagayowar ranar Arba’in na Imam Husaini {a.s}, sannan kuma ya taya wadanda suka halarci bikin “Makon Gwamnati”, inda ya bayyana fatansa cewa, wannan karo na shekaru goma sha hudu na hidimar gwamnati, ya kasance mako mai cike da fata da bushara kuma ya kasance yana dauke da rahotanni masu kyau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments