Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce nasarar da sabon zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian wajen gudanar da ayyukansa nasara ce ta dukkanin al’ummar Iran.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan majalisar sabuwar majalisar dokokin kasar Iran a yau Lahadi a birnin Tehran.
“Shawarata mai karfi ita ce kyakkyawar huldar majalisa da sabuwar gwamnati. Nasarar shugaban kasa da sabuwar gwamnati nasara ce ta mu baki daya. Ya kamata kowa ya taimaki shugaban kasa domin ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ga kasa,” inji shi.
Jagoran ya bayyana cewa idan shugaban kasa ya samu nasarar tafiyar da al’amuran kasar, inganta tattalin arziki, inganta huldar kasashen waje da al’adu, dukkanmu mun samun nasara. Nasararsa nasara ce a gare mu baki daya”.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da yin kira ga majalisar dokokin kasar Iran da hukumomin kasar da kuma jami’an kasar da su kasance da “hadin kai” wajen tunkarar muhimman batutuwa domin haifar da yanke kauna ga masu neman haifar da sabani a tsakaninsu.
A halin da ake ciki kuma, Jagoran ya bukaci majalisar da ta gaggauta baiwa majalisar ministocin kasar kuri’ar amincewa da Pezeshkian zai sanar, yana mai cewa, “Da zarar an amince da majalisar ministocin da aka gabatar, kuma gwamnati ta fara aiki, hakan zai kyautata lamurra a kasar.”