Search
Close this search box.

Jagora:  Ya Bukaci Mabiya Mazhabar Ahlul-Baiti(a)  Su Yada Mazhabar A Kasashen Duniya

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminaee, ya bayyana cewa nauyi ne a kan mabiya mazahabar iyalan gidan manzon

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminaee, ya bayyana cewa nauyi ne a kan mabiya mazahabar iyalan gidan manzon All..(s) ko shi’a su gabatar da mazhabar ga dukkan mutane a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagorana yana fadar haka a lokacinda tawagar malamai wadanda suka shirya taron Imam Riza (s) karo 5 a wannan shekara a birnin Mashahd suka ziyarceshi.

Jagoran ya kara da cewa dole ne yan shia su watsa shi’anci da dukkan manya manyan bangarorin mazhabar  wadanda suka hada da rayuwar limamansu, bangaren sanin All..sannan ilminsu sannan harkokin siyasan da suka jagoranta.

Ya ce sau da dama wasu sukan dauki wani bangare na rayuwar limamai(a) su rike, amma su bar sauran bangarorin, musamman bangaren siyasa.

Daga karshe ya jaddada bukatar a watsa al-amuran limamai masu tsarki ga kasashen duniya don su sani, matukar sun sansu to kuwa zasu bi su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments