Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Aya. Sayyid Aliyul Khamina’ie ya bayyana cewa yakin da kafafen yada labarai suke yi da makiya, ya dara na makamai da makiya idan an kwatanta bangarorin biyu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani sakon da ya aika a taron kafafen yada labarai wanda aka gudanar a yau a cikin hukumar gidajen radiyo da talabijin na kasar Iran IRIB a nan Tehran.
Jagoran ya kara da cewa korewa wajen bayyana gaskiya da kuma isar da sako ga mutane a duniya, sau da dama yafi yaki da makami, don isar da gaskiya ga mutane. Don haka ya bukaci hukumar gidajen radiyo da talabijin ta kasa ta dukufa wajen kyautata ayyukan ya da labarai a kasar, don isar da sakon JMI ga mutanen kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya.
Jagoran yace: Kun san da irin rawar da kafafen yada labarai suke takawa a duniya a yau. Musamman a fagen farfaganda a wannan zamanin. Akwai bambanci sosai tsakanin yaki da kafafen yada labarai suke yi, da kuma yaki da makami.
Imam Khamina’e ya kammala da cewa: A yau nasarar ta na samuwa ne da irin korewar da kasa take da shi wajen isar da sakon gaskiya ga mutane a duniya. Don haka dole ne mu ninninka karfimmu wajen amfani da kafafen yada labarai.