Jagora: Isra’ila ta gaza yin nasara kan Hamas da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada gazawar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila wajen karya lagon gwagwarmayar Palastinawa, duk kuwa da samun

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada gazawar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila wajen karya lagon gwagwarmayar Palastinawa, duk kuwa da samun gagarumin goyon baya daga bangaren Amurka da sauransu.

“Karfin tsayin daka yana kara fitowa fili a kowace rana,” in ji jagora a cikin wani sakonsa da aka wallafa a cikin harshen  Ibrananci a dandalinsa na X.

 Gwamnati mai karfin soji, siyasa, da tattalin arziki, kamar Amurka, tana mara baya da dukkanin karfinta ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila wajen yakar Hamas, amma sun kasa durkusar da su.”

Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ne dai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a kan zirin Gaza, da sunan tana mayar da martani kan ramuwar gayya da Hamas ta kaddamar da sansanonin sojin yahudawa, farmakin mai taken guguwar al-Aqsa.

Hare-haren wuce gona da iri ya zuwa yanzu ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 39,670, galibinsu mata da kananan yara.

Tun bayan da aka fara yakin, kungiyoyin gwagwarmayar daga kasashen Lebanon, Iraki, da Yemen su ma suke ci gaba da kai hare-hare masu ban tsoro a kan Isra’ila, domin tallafa wa al’ummar Gazan da ke fuskantar kisan kare dangi daga yahudawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments