Jagora: Iran za ta ci gaba da bin tafarkin hadin kan yankin duk da rashin Shugaba Raeisi

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce Iran za ta ci gaba da karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninta da kasashen

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce Iran za ta ci gaba da karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninta da kasashen yankin, duk kuwa da rashin shugaba Ibrahim Raeisi.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, wanda ya kai ziyara Tehran domin karrama marigayi shugaban kasar, wanda jagoran ya bayyana a matsayin “babban jigo a jamhuriyar Musulunci”.

Ayatullah Khamenei ya ce kasashen yankin ba su da wani zabi illa su hada kai wajen tunkarar yunkurin da ake yi na kawo cikas ga zaman lafiya a daukacin yankin.

A nasa bangaren Sarkin Qatar ya ce; dangantaka tsakanin Iran da Qatar ta kasance mai karfi kuma za ta ci gaba da wanzuwa a haka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments