Jagora: Dole ne a gurfanar da dukkan jami’an gwamnatin sahyuniya masu laifi

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi kira da a hukunta dukkanin jami’an siyasa da na soja na gwamnatin ‘yan ta’adda

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi kira da a hukunta dukkanin jami’an siyasa da na soja na gwamnatin ‘yan ta’adda ta  haramtacciyar kasar Isra’ila kan irin ta’asar da suka aikata.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sakonsa  da aka wallafa a cikin harshen Ibrananci a dandalin  X.

“Dole ne a gurfanar da dukkan manyan jami’an siyasa da na sojen, gungun ‘yan ta’addan sahyoniya masu laifi,” in ji jagoran.

An wallafa wannan sakon ne a daidai lokacin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ke ci gaba da kaddamar da yakin kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, da kuma yadda gwamnatin yahudawan ke ci gaba da kai hare-hare kan kasar Labanon, da kuma kisan gillar da ta ke yi a duk fadin yankin kudancin Asiya wanda ya hada da kasashen Siriya Iraki Iran da kuma Yemen, hare haren da suka kai ga shahadar manyan kwamandojin gwagwarmaya.

Yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 44,176, galibinsu mata da kananan yara, tare da raunata wasu 104,473, a Gaza kadai, a yayin da rikicin ya yi sanadiyar shahadar  mutane sama da 3,645 a kasar Lebanon.

Hare-haren na  gwamnatin yahudawan sahyuniya dai sun yi sanadiyar shahadar manyan jagororin gwagwarmaya irinsu Ismail Haniyeh, tsohon shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, da kuma tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, da kuma tsohon shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar Sayyed Hashem Safiyuddin.

Kalaman na Imam Khamenei na zuwa ne bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta fidda sammacin kame firayim ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan yakinsa  Yoav Gallant kan laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments