Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a yayin ganawa da wakilan majalisar kwararru a safiyar Alhamis, ya yi ishara da irin ci gaba da jajircewa da kuma ci gaba da gwagwarmayar da kungiyoyin Hizbullah da Hamas suke yi, ya jaddada cewa, bisa la’akari da alkawuran da ba za a iya musantawa ba na taimakon Ubangiji da kuma irin abubuwan da kungiyar Hizbullah da Hamas suka yi a cikin shekaru da dama da suka gabata, hakan wata manuniya ce da ke tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya a kan manufofinsu na gaskiya.
Kuma tabbas da suka faru na baya-bayan nan ko shakka babu, bababr manuniya ce a kan cewa za su kai ga cin nasara da kuma dakile hankoron gwamnatin Haramtacciytar Kasar Isra’ila na cimma burinta da manufofinta, wanda ta shelanta a matsayin su ne babban burinta na kaddamar da wannan yaki a kan al’ummomin Gaza da Lebanon.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya yi ishara da ayyukan yaki da zubar da jini da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi a Gaza da Lebanon da cewa, a fili take cewa akwai hannun Amurka dumu-dumu da kuma wasu kasashen Turai a cikin wannan ta’asa ta laifukan yaki, sannan kuma duk da wannan hadin gwiwa da taron dangi da Israila da kawayenta suka yi wa al’ummomin Gaza da Lebanon, sakamakon gwagwarmayarsu da tsayin dakansu, makiyansu sun kasa cimma bakaken manunfofinsua kansu, domin babbar manufar Isra’ila da Amurka da sauran ‘yan korensu daga cikin kasashen turai ita bayan ganin gwagwarmayar al’ummomin Falastinu da Lebanon, wanda kuma hakan bata tabbata ba, kuma ba za su taba yin nasara kan hakan ba.
Jagoran ya kara da cewa, duniya da kuma yankin gabas ta tsakiya za su ga wata rana da wadannan mujahidai za su yi galaba a kan gwamnatin yahudawan Sahyuniyawa.
Jagoran ya yi nuni da cewa, a tsawon tarihi gawgwarmayar al’ummomi masu gwagwarmaya a kan tafarkin gaskiya da neman adalci ne ke yin nasara, kuma har kullum Allah yana tare da masu gaskiya, ba azzalumai da masu cutar da bayinsa ba, saboda haka wannan shi ne babban dalili na nasarar mujahidai a yakin da suke gwabzawa da yahudawan sahyuniya.
Ya kara da cewa, a cikin shekaru kusan 40 da suka gabata, kungiyar Hizbullah ta tilastawa gwamnatin sahyoniyawan ja da baya daga wurare daban-daban, daga garuruwan Beirut, Sidon, da Taya, daga karshe kuma ta tilasta Isra’ila janyewa daga kudancin kasar Labanon, tare da ‘yantar da garuruwa, kauyuka, da yankunan kasar Lebanon daga mamayar yahudawan Haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ayatullah Khamenei ya bayyana kungiyar Hizbullah a matsayin kungiya mai karfi wadda ta samu babban ci gaba a fagen gwagwarmayar da take yi da gwamnatin sahyoniyawa, yana mai cewa: Duk da kasancewar manya manyan mutane irin su Sayyid Hassan Nasrallah da Sayyid Safi al-Din kungiyar Hizbullah ta rasa, amma ruhin mujahidai na wannan kungiya bai yi sanyi ba kuma zuciyarsu ba ta karaya ba kamar yadda kowa hatta makiya sun sheda hakan bisa abin da suke gani a fagen daga daga mayan Hizbullah, ta yadda suke ganin cewa yin nasara wajen murkushe ko gamawa da Hibzullah ba abu ne mai yiwuwa ba.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da haduwar wadannan ranaku na cika kwanaki arba’in da shahadar Sayyid Hasan Nasrallah, tare da sauran wadanda suka yi shahada tare da shi daga cikin manyan kwamnadoji da kuma wadanda suka yi shahada kafinsa ko bayansa, wadanda suka hada da Shahid Ismail Haniyeh, Sayyid Safi al-Din, Yahya Sinwar, da Nilforoushan, inda Jagoran ya bayyana cewa wadannan shahidai sun baiwa Musulunci da bangaren gwagwarmayar tabbatar da adalci ggarumar gudunmawa da kuma sadaukar da rayuwarsu domin wannan manufa.
Ya kira Hizbullah a matsayin wani gini mai karfi da Sayyid Hassan nasarallah ya gina, sanann kuma ya ce: Hizbullah ta samu ci gaba mai ma’ana sakamakon jajircewa, tsantseni, hakuri, da dogaro da Allah, da kuma jagoranci mai ban mamaki na Sayyid Nasarallah, wanda ya kasance bisa mahanga ta ilimi da masaniya da gogewa da tsoron Allah.
A bangaren Falastinawa kuwa, Jagoran ya ci gaba da cewa: akwai nasarorin da ake samu game da gwagwarmayarsu wadda ta dauke tsawon shekaru masu yawa suna yi, domin kwatar ‘yancin kansu da na al’ummarsu, da kuma kare martabar wurare masu tsarki na dukkanin addinai da aka saukar daga sama da suke cikin Falastinu.
Babban misalign hakan shi ne yadda aka fafata tsakanin mujahidai a Gaza da Haramtacciyar kasar Isra’ila har sau 9 tun daga daga shekara ta 2009, kuma har inda yau take ba su gajiya ko mika wuya ga yahudawa ba, saboda imanin da suke da shi kana bin da suke yi, wanda ya ratsa zuciyarsu kuma suka gina manufarsu a kansa.
Ayatollah Khamenei ya bayyana gwagwarmayar Falastinawa da cewa ita ce ta yi nasara, babban dalilin hakan kuwa shi ne, yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kasa kawo karshen wannan gwagwarmaya , a madadin hakan ne sai koma kashe mata da kananan yara da tsoffi da rusa gidaje da masallatai da kasuwanni da makarantu da asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da na bayar da agaji da makamantan hakan, wanda hakan a fili gazawa da yanke kauna daga samun nasara a kan gwagwarmayar al’ummar Falastinu.