Isra’ila Zata Gamu Da Maida Martani Mai Tsanani Idan Ta Kuskura Ta Sabonta Yaki Da Iran

Babban hafasan hafsoshin kasar Iran Major General Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta sabonta yaki da kasar Iran ta zata fuskanci

Babban hafasan hafsoshin kasar Iran Major General Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta sabonta yaki da kasar Iran ta zata fuskanci maida martani mafi tsanani.

Janar Musawi ya bayyana haka ne a jiya laraba a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta almayaden ta kasar Lebanon

Ya kuma kara da cewa a yakin da ya gabata wato wa’adussadik na ukku na watan da ya gabata, sojojin Iran basu fitar da dukkan makamansu su. Ko kuma dukkan karfinsu ba. Don haka idan yahudawan sun  kukura sun sake farfado da yaki da JMI sai sun hadu da martani wanda ya fi na farko zafi,

Janar Musavi ya kara da cewa HKI ta dauki shekaru tana tanajin ranar da yaki zai hadata da JMI, kuma ta ga inda tanadinta yak are. Ya ce abinda yake gaba gareta ya fi muni idan bata sani ba ta sani.

A wabi bangare Janar Musawi ya bayyana cewa kasashen yamma da kuma HKI sun son amfani da shirin makamashin nukliya na kasar Iran don raba kasar Iran da kuma maida ita fiye da yadda take a zamanin nsarki sha. Amma tare da taimakon All..sun kasa yin haka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted