Sojojin Isra’ila sun kashe wasu yara falasdinawa guda biyu a yankin gaza duk da yajejejeniyar dakatar da bude wuta da a sanya hannu akai, da ta fara aiki a farkon watan oktoba kamar yadda hukumar unicef tayi gargadi akai.
Tun da aka rattaba hannun kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a ranar 11 ga watan oktoba, akall yara dubu 67 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren isra’ila a yankin Gaza, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, wannan shi ne kididdigar da aka fitar dake nuna cewa kullum isra’ila na kashe yara biyu a kullum
Kakakin hukumar kula da kana nan yara na majalisar dinkin duniya yayi gargadi game da matsanancin halin dubban daruruwan yara falasdinawa za su shiga a lokacin hunturu.
Har iya yau ya kara da cewa daga sanda isra’ila ta kaddamar da hari a yankin gaza a watan oktoban shekara ta 2023 ta kashe falasdinawa sama da 70,000 mafiyawancinsu mata ne da yara kanana, yayin da sama da mutane 1700,000 sun bata bat sama ko kasa.