A safiyar yau ne 8 Agustan 2024 ‘yan sandan gwamnatin sahyoniyawan suka haramta wa Sheikh Ikrama Sabri mai limamin masallacin Aqsa shiga wannan masallaci mai alfarma da harabarsa na tsawon watanni 6.
Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, “Khaled Zabarqa” lauyan Sheikh Ikrama Sabri ya bayyana dangane da haka cewa: ‘Yan sandan Isra’ila sun yanke shawarar kame mai wa’azin masallacin Al-Aqsa kuma shugaban majalisar koli ta Kudus tare da haana shi shiga masallacin ko harabarasa har tsawon watanni 6, saboda Ta’aziyyar shahadar Ismail Haniyya da ya yi.
Ya kara da cewa: An dauki wannan matakin ne bayan wani gagarumin gangami na tsokana da yahudawa masu tsatsauran ra’ayi kan matsayin Sheikh Sabri dangane da kisan Haniyya.
Zabarqa ya ce: Maganar mai wa’azi a masallacin Al-Aqsa ba ta sabawa hatta dokokin gwamnatin sahyoniyawan ba, kuma abu ne da ya dace mutum irin Sheikh Ikrame Sabri ya jajanta kan shahadar wani babban shugaba na wani muhimmin bangare na Palasdinawa da ke a matsayin jigo na al’ummar Falasdinu.
A ranar Juma’a 2 ga watan Agusta ne sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka kashe Sheikh Ikrame Sabri (mai shekaru 84) bayan da suka kai hari a gidansa da ke unguwar “Al-Swanah” da ke birnin Kudus da Isra’ila ta mamaye, bayan da ya yi jawabi a cikin hudubar sallar Juma’a da ya yi kan shahadar Ismail Haniyeh.
Kamen Sheikh Sabri dai ya biyo bayan kiraye-kirayen yahudawan sahyoniya, ta yadda da yawa daga cikin ministocin gwamnatin yahudawan da kuma wasu daga cikin ‘yan majalisar Knesset suka bukaci a kama limamin masallacin na Al-Aqsa tare da kwace shaidarsa ta limanci, da kuma takardu na shaidar zama dan kasa.