Isra’ila ta hana tawagar kasashen Larabawa shiga gabar yammacin kogin Jordan

Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye

Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah.

Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa.

Wani jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta CNN a ranar Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ba za ta hada kai da hukumar Falasdinu ta PA ba da ke neman karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya.

Jami’in ya bayyana ziyarar a matsayin tsokana, yana mai cewa “Isra’ila ba za ta hada kai da irin wannan mataki da nufin cutar da Isra’ila ba.”

A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa da shugaban hukumar Falasdinu Mahmoud Abbas, a cewar Hussein al-Sheikh, mataimakin shugaban hukumar ta PA.

Wannan dai za ta kasance ziyara mafi girma da Saudiyya za ta kai yankin tun bayan da Isra’ila ta mamaya yankin a shekarar 1967.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ke kokarin ganin kasashen duniya su amince da Falasdinu a matsayin kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments