Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta

Hukumar bada agaji da samar da ayyukan ga falasdinawa na majalisar dinkin duniya UNRWA ta fadi cewa isra’ila ta hana motoci makare da kayan agaji

Hukumar bada agaji da samar da ayyukan ga falasdinawa na majalisar dinkin duniya UNRWA ta fadi cewa isra’ila ta hana motoci makare da kayan agaji guda 6000 shiga yankin Gaza da suke dauke  da abinci magunguna da za su iya wadatar da yankin na tsawon watanni 3.

Kakakin kungiyar ta UNRWA Adnan Abu Hasna ya fadi cewa duk da yake cewa adadin kayan da ake shiga da shi yankin gaza ya karu tun bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta a watan oktoba, sai dai duk da haka isra’ila ta hana shigar da kayayyakin da ake bukata da zasu iya taimakwa wajen warware matsalar da yankin ke fuskata.

A watan oktoba isra’ila ta shaidawa majalisar dinkin duniya cewa za ta bari motoci dauke da kayan agaji guda 3000 su shiga yankin gaza inda suka raba adadin zuwa gida biyu, jiragen Ruwan da Isra’ila ta kama suna dauke da dubban tanti da barguna da aka kiyasta za su kai guda 1.3 domin rabawa wadanda aka rusa gidajensu a fadin yankin.

Kungiyoyin bada agaji sun yi barazanar cewa Rashin sakin dubban kayayyakin daga isra’ila ya kara jefa yankin cikin mummunan bala’I da zai kara dagula alamura a yankin, inda Asibitoci bada aiki saboda babu kayan aiki, mutane da ake rusa gidajensu basu da wajen zama, kuma cututtuka na yaduwa kamar farin dango a yankin gaza

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments