Isra’ila ta hana ayarin motocin agaji na arewacin Afrika shiga Gaza

Ministan yakin Isra’ila, Israel Katz, ya umarci sojojin kasar da su hana ayarin motocin agaji na arewacin Afirka shiga yankin Zirin Gaza da aka yi

Ministan yakin Isra’ila, Israel Katz, ya umarci sojojin kasar da su hana ayarin motocin agaji na arewacin Afirka shiga yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

A cikin wata sanarwa ofishin Katz ya umarci sojojin Isra’ila da su hana “masu fafatuka daga Masar shiga yankin Zirin Gaza.

Katz bukaci “Hukumomin Masar dasu hana zuwan masu fafatukar a kan iyakar Masar da Isra’ila.”

Ministan ya ya bayyana hakan a matsayin hadari ga jami’an tsaron Isra’ila na IDF.”

Wannan dai na zuwa ne bayan ayarin motoci 100 da ya kunshi dubban masu fafatuka daga kasashen Morocco, Aljeriya, Tunisia, Libya da Masar, suka yunkuri anniyar wayar da kan al’ummar duniya kan matsalar jin kai a Gaza, da neman kawo karshen yakin kisan kare dangi, da karya shingen da Isra’ila ke yi da kuma kai muhimman kayayyakin jin kai a Gaza.

Ayarin da ya kunshi kungiyoyin kwadago da masu fafutukar kare hakkin bil’adama da ‘yan wasa da lauyoyi da likitoci da ‘yan jarida da na kungiyoyin matasa da dai sauransu ana sa ran za su shiga Masar a yau Alhamis kafin isa mashigar Rafah da ke kan iyaka a kudancin zirin Gaza.

Kafin hakan dama sojojin Isra’ila sun kwace jirgin ruwan agaji na Madleen da ke kan hanyarsa ta zuwa Gaza domin kai tallafi ga al’ummar Zirin, bayan shafe sama da watanni ashirin na yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi.

An kama dukkan masu fafutukar na kasa da kasa su 12 da ke cikin jirgin, ciki har da mai fafutukar Sweden Greta Thunberg.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments