Isra’ila Na Ci Gaba Da Kaddamar Da Hare-Haren Kisan Kare Dangi Kan Al’ummar Gaza

Sojojin Isra’ila na ci gaba da kaddamar da munan hare-haren kisan kare dangi kan al’ummarv yankin zirin Gaza. Rahotannin sun tabbatar da cewa, sojojin Isra’ila

Sojojin Isra’ila na ci gaba da kaddamar da munan hare-haren kisan kare dangi kan al’ummarv yankin zirin Gaza.

Rahotannin sun tabbatar da cewa, sojojin Isra’ila sun kara tsananta hare-haren nasu ne tun bayan da shugaban kasar Amurka ya gabatar da shawarar dakatar da bude wuta, inda gwamnatin yahudawan tace tattaunawar sulhu ba zata hana ci gaba da yakin ba.

Hare-Haren an Isra’ila dai sun fi tananta nea  kan gidajen jam’a, da kuma cibiyoyin da aka tsugunnar da mutanen da suka kauracewa muhallansu domin tsira da rayukansu, da hakan ya hada da sansanoni na majalisar dinkin duniya, da makarantu da asibitoci da makamantansu.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kiyashi kan yankin Zirin Gaza, wanda ke karkashin kulawar Hamas, bayan da kungiyar ta Hamas ta kaddamar da wani farmakin ramuwar gayya kan ayyukan cin zarafi da wuce gonad a iri na Isra’ila a yankunan Falastinawa.

Akalla Falasdinawa 36,550 aka kashe, yawancinsu mata da kananan yara, sannan wasu 82,959 kuma suka samu raunuka a yakin. Fiye da mutane miliyan 1.7 daga cikin mutane miliyan 2.4 da suke rayuwa a Gaza ne suka rasa matsugunansu sakamamkon munanan hare-haren Isra’ila a yankin.

Masar da Qatar dai na shiga tsakani a tattaunawar da ake yi da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Nuwamba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments