Search
Close this search box.

Isra’ila : An Yi Zanga-zangar Matsin Lamba Wa Gwamnati Ta Cimma Yarjejeniya Da Hamas

A Isra’ila zanga zanga ce aka gudanar a fadin kasar jiya Lahadi, domin matsin lamba wa gwamnatin kasar akan ta cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas.

A Isra’ila zanga zanga ce aka gudanar a fadin kasar jiya Lahadi, domin matsin lamba wa gwamnatin kasar akan ta cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas.

An fara zanga zangar ne da misalign karfe 06H29 lokacin da mayakan Hamas suka soma kaddamar da hari a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Masu zanga-zangar na bukatar gwamnatin kasar ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta don tabbatar da sakin Isra’ilawan ake garkuwa dasu a daidai lokacin da yakin da Isra’ila ta shelanta bayan harin na Hamas ya shiga watan sa na goma.

Masu zanga-zangar sun yi ta toshe tituna tare da hana ministocin gwamnati shiga gidajensu.

A kwanakin baya-bayan nan ne dai fatan cimmar yarjejeniyar ya taso, duk da cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare cikin Gaza.

Nan gaba kuma a gobe ne ake sa ran tawagar masu shiga tsakani na Isra’ila karkashin jagorancin shugaban kungiyar Shin Bet Ronen Bar za ta tashi zuwa birnin Alkahira, yayin da ake ci gaba da tattaunawa dan sasantawa domin kawo karshen yakin Gaza, in ji wani babban jami’in Isra’ila da bai bayyana sunansa ba.

An sake farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Isra’ila da Hamas a makon da ya gabata inda masu shawarwarin Isra’ila suka shiga tattaunawar a Doha ranar Juma’a. Farfadowar ta zo ne a daidai lokacin da Netanyahu ke fuskantar matsin lamba na cikin gida kan yakin Gaza, ciki har da ta iyalan wadanda Hamas ke tsare da su da kuma na manyan jami’an soji, kamar yadda kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments