Jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a MDD ya yi watsi da tuhume-tuhumen da Amurka da Birtaniya suke yi wa Iran akan abubuwan da suke faruwa a tekun “Red Sea’ da Yemen.
Amir Sa’id Iruwani ya rubuta wasika zuwa shugaban kwamitin tsaro na MDD a jiya Litinin da a ciki ya kore dukkanin zarge-zargen da a ka yi wa Iran a yayin zaman kwamitin tsaro na ranar 14/ Maris/2024.
Iruwani ya kuma ce; Abin takaici ne cewa wakilan Amurka da Birtaniya sun yi amfani da wannan zaman inda su ka dora wa Iran alhakin abinda yake faruwa a tekun “Red Sea’alhali babu tushe a cikin abubuwan da su ka ambata.
Wakilin na Iran a kwamitin tsaron ya kuma ce; Iran ba ta lamunta da wadannan zarge-zargen ba tun daga tushensu, kuma Washington da London suna son yin amfani da hakan ne domin shimfida siyasarsu, da kuma halarta wa kansu hare-haren da suke kai wa Yemen.