IRIB Ta Kaddamar Da Tashoshin Talabijin Ta Presstv- Turkanci, Da Kuma HispaTV Potigal

Shugaban hukumar tashoshin Radiyo da talabijin na kasar Iran Peyman Jebelli ya kaddamar da tasoshin talabijin na Presstv Turkancin-Istambul da kuma Hispa Tav ta kasar

Shugaban hukumar tashoshin Radiyo da talabijin na kasar Iran Peyman Jebelli ya kaddamar da tasoshin talabijin na Presstv Turkancin-Istambul da kuma Hispa Tav ta kasar Barazil mau watsa shirye shiryensu da harsunan Turkanci da kuma Potigal.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jebilla yana fadar haka a wani taro a nan Tehran don kaddamar ta tashoshin talabijan guda biyu.

A jawabinsa a taron Jebilli ya kara da cewa tare da kaddamar da wadannan tashoshin talabijin guda biyu JMI ta kara fadada fagagen watsa labaranta a duniya.

Ya ce kaddamar ta Presstv Turkanci ya kara dankon zumunci tsakanin Iran da mutanen kasar Turkiyya saboda watsa shirye shirye da harshen Turkancin Istambul daga kasar Iran. Yace wannan zai sa mutanen kasar Turkiyya su fahinci JMI da kuma matsatinta a yankin da kuma duniya.

Jebilli ya kara da cewa Hispa TV ta dade tana watsa shirye shiryensa da harshen Espaniyanci, amma a halin yanzu an kara yaren potigal.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments