Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran IRGC sun bada labarin fadawar makamai masu linzamunsu kan sansanonin rundunar CENCOM na Amurka a kasar Jordan.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ta IRGC na cewa, makaman sun fada kan sansanin sojojin sama na Amurka da ake kira Muwaffaq Salti Air Base a kasar Jordan. Sannan ta kara da cewa duk wani karin hare hare kan kasar Iran zai jawo maida martani mafi tsanani daga bangaren IRGC.
Majiyar ta kara da cewa sun yi amfani da makamai da dama daga ciki har da makamai masu linzami bilistic har guda 10 a wadan nan hare hare, kan sansanin sojoji na Al-Azrag. ‘Nasara daga All..ce shi kadai’ inji IRGC.