Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran, Hossein Salami, ya yi barazanar cewa za su kai wa Isra’ila hari “da zafi” idan ta kuskura kai hari kan Iraniyawa a matsayin mayar da martani ga hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai a ranar 1 ga Oktoba.
A wani jawabi mai karfi a wajen jana’izar Manjo Janar Abbas Nilforoushan a Isfahan, babban kwamandan IRGC, Manjo Janar Hossein Salami ya yi wani kakkausan gargadi ga jami’an Isra’ila, yana mai cewa “Operation True Promise 2” gargadi ne kawai.
Janar Salami, ya bayyana hakan ne a yayin jana’izar Nilforoushan wani babban hafsan tsaron kasar da ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai wanda kuma ya yi sanadiyyar shahadar tsohon shugaban kungiyar Hizbullah, Hassan Nasrallah, a karshen watan Satumba a Lebanon.
“Dole ne ku fahimci cewa lokacin da kuka kai wa ‘yan kasarmu hari, ko masu kishinmu, ko bukatunmu, za mu rama.”
Kalaman Salami na kara jaddada aniyar Iran na kare kanta a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da mayar da martani mai karfi kan barazanar da Isra’ila ke yi, lamarin da ke nuni da cewa sojojin Iran ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan kare al’ummarta da ‘yancinsu.