Gwamnatin Ireland ta bi sahun Afirka ta Kudu a hukumance kan shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa ta ICJ, da ke tuhumar Isra’ila da aikata laifukan kisan kiyashi a Zirin Gaza.
A ranar Laraba ne gwamnatin Ireland ta amince da matakin shiga cikin lamarin. Ministan harkokin wajen kasar, Micheál Martin, ya bayyana cewa shigar Ireland na da nufin kara tabbatar da laifin kisan kiyashi da wata kasa ta yi.”
Martin ya bayyana damuwarsa kan yadda ake fassara ma’anar kisan kiyashi a halin yanzu, yana mai cewa, “Matakan da ake dauka wajen baiwa kisan kiyashi wata fassara ta daban, yana haifar da rashin hukunta masu laifi, inda ake tauye hakkin fararen hula.”
Ireland ta shiga cikin kawancen kasashe masu goyon bayan Afirka ta Kudu, da suka hada da Brazil, Turkiya, Malaysia, Chile, Spain, Pakistan, da Syria.
Tun da farko Afirka ta Kudu ta shigar da karar ne a watan Disambar 2023, inda ta yi zargin cewa ayyukan mamayar da Isra’ila ke yi a Gaza ya saba wa yarjejeniyar kisan kare dangi ta 1948.
A cikin Janairu 2024, kotun ICJ ta amince da “hadarin kisan gilla a Gaza” da kuma ci gaba da cutar da fararen hula amma kuma ba ta bayar da umarnin tsagaita wuta ba. Sai dai kotun ta umurci haramtacciyar kasar Isra’ila da ta dauki dukkan matakan da suka dace don hana ci gaba da kisan kare dangi.
Ireland ta ce ta shirya shiga cikin karar da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra’ila a kotun kasa da kasa (ICJ) a karshen wannan shekara.