Ministan kudi na kasar Iran ya bayyana cewa zuba jari daga kasashen a cikin shekaru uku na gwamnatin shugaba Shahid Ibrahim Ra’isi ya ninninka hatta na zamanin da yarjeniyar JCPOA take aiki a kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ehsan Khandouzi ministan kudi na kasar Iran yana fadar haka, ya kuma kara da cewa a cikin shekaru uku na gwamnatin shugaban Ra’isi an sami kamfanonin kasashen waje wadanda suka zuba jari a kasar ninki biyu idan an kwatanta da zamanin da aka dagewa kasar takunkuman tattalin arziki wato bayan yarjeniyar JCPOA.
Ehsan Khandouzi ya kara da cewa a tarihin kasar a cikin shekaru uku da suka gabata ne aka sami zuba jari daga kasashen waje hard a dalar Amurka biliyon 5.5.
A shekara ta 2015 ne manya manyan kasashen duniya masu kujerun din din din a kwamitin tsaro na MDD da kuma kasar Jamus wato P5+1 suka rattaba hannu kan yarjeniyar shirin makamashin nukliyar kasar Iran wanda aka fi sani da JCPOA, sannan kwamitin tsaro ya sake samar da kuduri mai lamba 2231 wanda yake goyon bayan yarjeniyar, daga nan ne aka daukewa kasar takunkuman da MDD da kuma kasashen yamma suka dora mata. Sai dai shugaba Turm ya yi watsi da wannan yarjeniyar a ranar 18 ga watan Mayun shekara ta 2018 shekaru kimani 3 da yarjeniyar ya kuma kara tsananta takunkuman tattalin arziki kan kasar ta Iran.
Ministan ya kara da cewa yawan zauba jari daga kasar waje a zamanin shugaba shahid Ra’isi ya kai dalar Amurka biliyon 12. Yace a gaban ta tsakiya dai kasar Iran tana daga cikin kasashen da suka fi samun zuba jari daga kasashen waje a wannan shjekarar. Banda haka a shekara ta 2022 iran ce kasa ta 4 daga cikin kasashe 10 na yankin a bangaren zuba jari kai tsaye daga kasashen yanbkin.