Iran: Zaben Kasar Venezuela Yana Nuni Da Hakikanin Tsarin Demokradiyya

 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Msuulunci ta Iran Dr.Nasir Kan’ani ya wallafa a shafinsa na “X” sakon taya murna ga shugaba Nicolas Maduro da aka

 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Msuulunci ta Iran Dr.Nasir Kan’ani ya wallafa a shafinsa na “X” sakon taya murna ga shugaba Nicolas Maduro da aka sake zabarsa a wani karo a matsayin shugaban kasar Venezuela, tare da cewa, saboda yadda mutane da dama su ka shiga yin zaben da kuma masu sanya idanu na kasa da kasa, yana a matsayin kyakkyawar shaida akan tsayuwar tsarin Demokradiyya a cikin kasar.

Dr. Kan’ani ya kuma kara da cewa; A kodayaushe jamhuriyar musulunci ta Iran tana goyon bayan kasar Venezuela a koakrinta na cigaba da, haka nan kuma bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu.

Shi dai Maduro ya sami kaso 51% na jumillar kuri’un da aka kada wanda aka sami ‘yan takara da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments