‘Yan takara biyu da ke neman shugabancin kasar Iran da za su kara a zabe zagaye na biyu Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, sun tafka muhawarar farko ta talabijin, domin gabatar da shirye-shiryensu kan batutuwan siyasa da tatatlin arziki da inganta rayuwar jama’a da ci gaban kasa.
Wannan shi ne karo na farko daga cikin muhawara biyu da za su tafka kafin zaben shugaban kasa wanda za a gudanar a ranar 5 ga watan Yuli, wanda kuma a yammacin Talata ne za a yi muhawara ta biyu.
A ranar Lahadi ne aka fara yakin neman zaben zagaye na biyu, kwana guda bayan sanar da sakamakon zaben na ranar 28 ga watan Yuni da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar.
Pezeshkian da Jalili ne suka samu mafi yawan kuri’un da aka kada a zaben, amma babu wani dan takara da ya iya samun cikakken rinjaye, wanda kuma hakan ne ya share fagen zuwa zaben zagaye na biyu.
Pezeshkian tsohon ministan lafiya ne kuma babban dan majalisa daga birnin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar, yayin Jalili kuma shi ne tsohon mai jagorantar shawarwarin nukiliyar Iran, kuma tsohon shugaban kwamitin tsaron kasa.