Iran: ‘Yan Takarar Shugabancin Kasa A Zagaye Na Biyu Sun Sake Tafka Muhawara

‘Yan takara biyu da ke neman kujerar shugabancin kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, sun fafata a muhawara ta biyu da aka watsa a

‘Yan takara biyu da ke neman kujerar shugabancin kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, sun fafata a muhawara ta biyu da aka watsa a gidan talabijin na kasar Iran kan zaben zagaye na biyu na shugaban kasa da za a gudanar a ranar Juma’a mai zuwa.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin muhawara guda biyu gabanin zaben zagaye na biyu, na shugaban kasa a ranar 5 ga watan Yuli, wanda kuma muhawarar ta fi mayar da hankali ne kan batutuwan tattalin arziki. A yammacin ranar Litinin ne aka gudanar da muhawara ta farko kan batutuwan siyasa da al’adu.

A ranar Lahadi ne kuma  aka fara yakin neman zaben zagaye na biyu a hukumance, kwana guda bayan sanar da sakamakon zaben ranar 28 ga watan Yuni da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar.

Pezeshkian da Jalili ne suka samu mafi yawan kuri’u amma babu wani dan takara da ya iya samun cikakken rinjaye, wanda ya share fagen zuwa zabe zagaye na biyu kamar yadda a cikin kudin dokokin zabe na kasar Iran.

Pezeshkian tsohon ministan lafiya ne kuma babban dan majalisa daga birnin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar. Yayin da Jalili kuma shi ne tsohon mai jagorantar shawarwari kan shirin nukiliyar kasar Iran, kuma tsohon babban sakataren majalisar tsaron kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments