Iran Tayi kira Da A Warware Rikici Tsakanin Afghnistan Da Pakistan Ta Hanyar Diplomasiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi kira ga kasashen biyu da su warware sabanin dake tsakanin ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya.

Iran ta dade tana ba da shawarwarin magance matsalolin tsaro a yammacin Asiya da kuma Kudancin Asiya, da kuma nuna rashin amincewa kan tsoma bakin kasashen waje kan rashin fahimtar dake tsakanin kasashen musulimi,  yace rikicin dake tsakanin Kabul da islam abad barazana ce ga zaman lafiya yankin, kuma zai amfanar da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi masu so su yi amfani da tarzoma a iyaka.

Rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan yayi Kamari a yan kwanakin nan inda ya jawo gwamman mutane suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, sai dai bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta na wucin gadi adaidai lokacin da hankula ke kara tashi da kuma tuhumar juna kan kai hare hare a iyakokin kasashen. Iran ta bayyana matsayar ta na shirin taimakawa ta kowanne bangaren wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro tsakanin kasashen musulmi guda biyu kuma abokai kuma makwabta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments