Shugaban kamfanin Sarrafa Sinadaran man fetur na kasar Iran ya bayyana cewa kasarsa tana son da kasance cikin wadanda zasu gina kamfanin sarrafa sinadaran man fetur na jumhuriyar Nijer, iran tana son ta taimaka wajen samar da takin zamani ga kasashen Afirka.
Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Hassan Abbaszadeh yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da ministan man fetur na Jumhuriyar Nijer a kasuwar baje kolin kayakin da aka kera a Iran wato Iran EXPO 2025 karo na 7 wanda aka kamala.
Abbaszadeh ya kara da cewa sinarin Urea wanda JMI take samarwa zai amfani amfani kamfanin sinadaran man fetur na kasar Nijer don samar da takin zamani wanda zai sami kasuwa babba a kasashen Afirka.
Shugaban kamfanin sinadaran man fetur na kasar Iran ya kamala da cewa Iran zatsa tsarawa jumhuriyar Niger, hanyar kaiwa ga samarda kamfanin sarrafa sinadaran man fetur a kasar a yayinda iya Iran zata sami kasuwa a nahiyar Afrika.
Daga karshen ministan man fetur na Nijer ya ce, Niger a shirye take ta sanya hannu a kan dukkan abubuwan da don tabbatar haka.