Iran Tana Saida Danyen Man Fetur Ga Kasashe 15, Sanan Samar Da Sanadaran Man Fetur Ya Kara Yawa

Ministan harkokin man fetur na kasar Iran Javad Owji ya bayyana cewa a halin yanzu kasar tana saida danyen man fetur zuwa kasashe 15 a

Ministan harkokin man fetur na kasar Iran Javad Owji ya bayyana cewa a halin yanzu kasar tana saida danyen man fetur zuwa kasashe 15 a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Owji yana fadar haka, a lokacinda yake jawabin hadin giwa da kakakin gwamnati a jiya Asabar.

Ya kuma kara da cewa, an sami ci gaban a zo a gani a bangaren samar da sinadaran man fetur da dangoginsa wato Perochemicals. Ya kara da cewa a cikin yan shekaru masu zuwa za’a bude cibiyoyin samar da Karin sinadaran man fetur a kasar.

Owji ya kara da cewa, a ko wace shekara ana samun Karin ton miliyon 10 na samar da sinadaran man fetur. Sannan daga tun miliyon 90 da muke samarwa a ko wace shekara a wannan shekara adadin zai karu zuwa ton miliyon 100.

Har’ila yau ministan ya kara da cewa yawan gas na amfanin gidaje ya kai cubic mita miliyon 11.5 a ko wace rana. Sannan kasar tana samun dalar Amurka biliyon 5 a ko wace shekara. Sannan a cikin shekaru shekaru uku da suka gabata yawansa ya karu da cubic mita miliyon 4.5.

Daga karshe ministan ya kamala da cewa, shugaban shahid Ra’isi ya bude wasu hanyoyin saida man fetur wanda zai karya takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments