Iran Tace Ta Gamsu Da Yadda Tattaunawarta Da Amurka Yake Tafiya Zuwa Yanzu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar a birnin Mascat na kasar Omman.

Ya ce bangarorin biyu a shirye suke su ci gaba da tattaunawa, ya kuma kara da cewa tawagra tattaunawa a wannan karon sun dan kara yawa, don akwai bukatar kwararrun a bangaren siyasa, sannan a zama mau zuwa a ranar Asabar mai zuwa zai hada kwararru a fanni makamashin nukliya.

Ministan ya kammala da cewa idan Amurka da gaske tana son hana Iran mallakar makaman Nukliya ne to yana da yakini kan cewa zamu kai ga yarjeniyar mai kyau. Ammam in ta shigar da wani ami zata samu matsala.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments