Ministan harkokin wajen JMI Abbas Aragchi ya bayyana cewa ba za’a taba samun zaman lafiya a duniya ba sai an warware rikicin da ke faruwa a yammacin Asiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ministan yana fadar haka a taron ‘United Nations Alliance of Civilizations Forum’ wato ‘kawance tsakanin ci gaban al-ummu’ karo na 10 a birnin Geneva.
Ya kuma zargi manya manyan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa a duniya, kan rashin tabuka kome a cikin watanni kimani 14 da suka gabata, don kawo karshen yakin fin karfin da HKI take yi a Gaza.
Aragchi ya bayyana cewa shekaru fiye da 70 da suka gabata ne HKI take kokarin shafe al-ummar Falasdinu daga kasarsu da ta mamaye, ya kuma kara da cewa, amma kasashen yamma sun ci gaba da goyon bayan ta a duk tsawon wadannan shekaru.
Kungiyoyin MDD kama daga kwamitin tsaro, kutunan ICJ da ICC duk sun kasa yin wani abu don kawo karshen mulkin mallakan da HKI takewa Falasdinawa.