Iran Ta Zabo Wuraren Maida Martani A HKI Idan Ka Kuskura Ta Kawo Mata Hari

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa sojojin kasar Iran a shirye suke su maida martani mai tsanani a kan HKI matukar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa sojojin kasar Iran a shirye suke su maida martani mai tsanani a kan HKI matukar ta kuskura ta kaiwa kasar hari kamar yadda ita da kawayenta suke yayatawa a kafafen yada labaran kasashensu a cikin yan kwanakin nan.

Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya a kasar Turkiyya inda yake ziyarar aiki na kwanaki biyu.

Aragchi ya ce: Wani hari kan kasar Iran wuce iyaka ne, Iran ba zata kyale shi ba tare da maida martani ba, musamman idan ta kai hare haren kan cibiyoyin nukliyar kasar. Yace: hare haren wa’adussadik na 2  a ranar 1 ga watan Octoban da muke ciki kan HKI, ya wargaza wurare tsaro masu muhimmanci a kasar,  kuma idan ta kuskura ta kawo hari kan Iran, sojojin kasar sun rike sun zabi wuraren da zasu maida martani a kan su a HKI.

Ya kuma kammala da cewa a hare haren wa’adussadik na 2 kashi 90% na wuraren da Iran take son makaman su fada sun fada kamar yadda ta tsara. Daga karshe yayi gargadin cewa, mai yuwa yakin nan ya yadu zuwa wasu kasashen yankin. Amma har yanzun akwai damar kawo karshen yakin ta hanyar tattaubawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments