Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da jami’an Birtaniya suka yi na cewa Tehran na barazana ga tsaron kasar ta Burtaniya.
A cewar jami’an Iran, Ingila na zargin Iran da wani abu da ta yi fice a kai.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya mayar da martani da kakkausan lafazi kan wannan zargi, yana mai cewa wannan maganar banza ce.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, ya tunatar da cewa ita kanta kasar Birtaniya kwarariya ce wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe.
A kwanakin baya ne sakataren tsaron Burtaniya Dan Jarvis ya gabatar da shawarar a gaban majalisar dokokin kasar cewa za a kara sa ido kan gwamnatin Iran da suka hada da jami’an tsaronta da kuma dakarun kare juyin juya halin Musulunci a karkashin wani sabon tsari don dakile barazanar.